Ferguson ba zai sayar da Nani ba

Image caption Sir Alex Fergson ba zai sayar da Nani ba

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Sir Alex ferguson, ya nanata cewa dan wasan nan Nani ba za a sayar da shi a watan Janairu mai kamawa ba duk da nuna sha'awar dan wasan da Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da Tottenham suka yi ba.

Nani mai shekaru ashirin da shida ya buga wasanni goma sha daya a Manchester united wannan kakar wasannin kuma kwantaraginsa za ta kare ne a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.

Ferguson ya ce har yanzu suna da bukatar Nani domin yanayin wasu abubuwa daban da wasu 'yan wasan.

Mai bada horon ya ce ba zai yi musayar 'yan wasa sosai ba a watan Janairun shekara mai zuwa saboda ya gamsu da wasan da tawagar sa suke buga masa.

Karin bayani