Rashin Van Persie asara ce —Mancini

Robin van Persie
Image caption Roberto Mancini ya ce Robin van Persie na da matukar muhimmanci ga Manchester City

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce gazawar kungiyar ta sayen Robin van Persie ka iya sanyawa ta kasa lashe Gasar Premier.

Mancini ya ce "saura kiris" ya sayi Van Persie, wanda ya ci kwallaye 14 a wasanni 20 bayan da Manchester United ta saye shi daga Arsenal a kan kudi fam miliyan 24.

A cewar Mancini, wanda kungiyarsa ke bin bayan United da maki bakwai, "Robin van Persie dan wasa ne mai matukar muhimmanci ga Manchester United; ya kawo musu sauyi, kuma shi ne ya bambanta su da mu".

Kafin ya koma United dai an alakanta Van Persie—wanda ya ci wa Arsenal kwallaye 37 a kakar wasanni ta bara—da City.

"Mun so mu sayi Van Persie saboda mun san cewa dan wasa ne mai matukar muhimmanci", inji Mancini, wanda ya kara da cewa, "Akwai bambanci sosai tsakaninsa da sauran 'yan wasanmu na gaba. Mun so mu saye shi saboda wasanninmu na Gasar Zakarun Turai da na Gasar Premier.

"Saura kiris mu saye shi watanni uku ko hudu kafin ya koma United".

Karin bayani