Andy Murray ya ce ya kara shiri

Andy Murray
Image caption Andy Murray ya kuma samu lambar zinare a Gasar Olympics ta 2012

Dan wasan tennis na Burtaniya Andy Murray ya ce yana jin a shirye yake fiye da da ya fuskanci ko wacce babbar gasa bayan da ya yi nasara a gasar US Open.

Murray, wanda ya kuma lashe lambar zinare a gasar Olympics ta 2012, shi ne ya kawo karshen jiran da Burtaniya ta jima tana yi na ganin wani danta ya lashe daya daga cikin manyan wasannin tennis na duniya lokacin da ya lallasa Novak Djokovic.

"A 'yan shekarun da suka gabata na sha kaiwa daf da yin nasara amma ban samu na tsallake matakin karshe ba", inji Murray.

Dan wasan na uku a duniya ya kara da cewa: "Yanzu da na samu sa'ar kai labari, ina fata idan na sake fuskantar irin wannan gasar zan fi taka rawa sosai".

Murray zai bude shekarar 2013 ne da fafatawa da John Millman a Gasar Brisbane International ranar Alhamis.

Wannan gasar ce za ta zama share-fagen tafiya Gasar Australian Open—gasar da Murray ya kai wasan kusa da na karshe a 2012—wacce za a fara ranar 14 ga watan Janairu.

Karin bayani