Tottenham na dakon shawarar Adebayor

Emmanuel Adebayor
Image caption Manajan kungiyar kwallon kafa na Togo, Didier Six ya roki Adebayor ya buga wa kasar wasa

Kulob din Tottenham ba shi da tabbaci ko dan wasan gaba, Emmanuel Adebayor zai koma Togo don buga wa kasar wasa, a gasar cin kofin zakarun Afrika.

Dan wasan mai shekaru 28 a duniya zai taka leda ne a gasar da za a bude ranar 19 ga watan janairun da muke ciki, a kasar Afrika ta Kudu.

Kuma hakan zai sa ba zai buga wasanni biyar na gasar Premier league da kulob dinsa zai buga ba.

Adebayor ya taimaka wajen cin nasarar da Spurs ta samu a kan Reading, a wasan da suka buga a ranar Talata, inda aka tashi da ci uku da daya.

Sai dai manajan kulob din, Andre Villas-Boas ya ce " Idan yana son ya tafi to za mu mutunta shawarar da ya dauka."

A baya-bayan nan ne Adebayor ya dan dakatar da buga wasa na kasa da kasa, saboda rashin fahimtar juna da ya samu da kungiyar kwallon kafa ta Togo, game da kudaden da ake biya na wasanni.

Kuma da dama ana ganin cewa tsohon dan wasan Manchester City, ba zai so ya koma kasarsa ba, gara ya zauna a White Hart Lane.