Blackburn Rovers ta sayi Josh King

Image caption Blackburn Rovers

Kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers ta sayi dan wasan gaban Norway, Josh King daga Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Kuob din dai ya biya wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba kan dan wasan mai shekaru ashirin wanda ya rattaba hannu ga kwantiragi zuwa shekara 2015.

Dan wasan King, ya kasance a Kulob din Blackburn a watan Nuwamba ya kuma zura kwallaye biyu a wasanni takwas da ya buga a gasar zakaru.

King, ya ce yana farin ciki kasancewarsa a kulob din.

Karin bayani