John Mensah na Ghana ya koma Stade Rennes

Image caption Tawagar 'Yan wasan Ghana

Dan bayan kasar Ghana John Mensah ya koma Kungiyar kwallon kafa ta Stade Rennes zuwa watanni shida, shafin yanar gizo na Kulob din na Faransa ne ya bayyana hakan.

Tsohon dan wasan Sunderland ya buga wasanni 67 ga Olympique Lyon tsakanin shekarun 2006 zuwa ta 2008.

Mensah, ba a saka shi a a tawagar 'yan wasan da za su bugawa Ghana gasar cin kofin Afrika ba a Kasar Afrika ta Kudu.

Karin bayani