Transocean zai biya tarar malalar mai a Amurka

Barack Obama
Image caption Kamfanin Transocean zai biya tarar malalar mai

Kamfanin nan mai hakar mai, dake da hedkwatarsa a Switzerland, Transocean, ya amince ya biya tarar dala biliyan daya da miliyan dari hudu, bisa hannun da yake da shi a matsalar malalar man nan mafi muni a tarihin Amurka.

Ma'aikatar sharia ta Amirka, ta ce kamfanin wanda ya mallaki wurin hakar mai na cikin teku na 'Deepwater Horizon' a turance, ya amsa laifi, sakamakon tuhumar shi da aka yi, bayan wasu ma'aikata goma sha daya sun hallaka a lokacin da wurin hakar man ya yi bindiga.

Tuni shi ma kamfanin hakar mai na BP ya amince ya biya tara ta dala biliyan hudu da rabi a kwanan baya.

Karin bayani