Kulob din Chelsea ya sayi Demba Ba

Demba ba
Image caption Demba ba

Chelsea ta sayi dan wasan Newcastle kuma dan kasar Senegal Demba Ba, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku da rabi.

Sai dai ba a bayyana kudin da aka sayi dan wasan ba.

Bayanai sun nuna cewa kwantiragin Ba a Newcastle ta hada da bashi damar tattaunawa da wani klulob idan aka taya shi kan fan miliyan bakwai.

Dan wasan na kasar Senegal, wanda ya koma Newcastle daga West Ham a watan Junin 2011, inda ya maye gurbin Daniel Sturridge, wanda ya bar Stamford Bridge zuwa Liverpool a wannan makon.

Ba mai shekaru 27 ya zira kwallaye 13 a kakar wasanni ta bana a Newcastle.

Zuwansa Chelsea zai taimaka wurin rage dogaron da aka yi a kan Fernando Torres wanda aka sayo kan fan miliyan 50.

Dan wasan na kasar Spain ya zira kwallaye 14 a kakar bana, sai dai bakwai kawai ya zira a gasar Premier.