Liverpool ta sha da kyar

karawar liverpool da mansfield
Image caption Liverpool ta sha da kyar a hannun Mansfield

Kungiyar liverpool ta sha da kyar a hannun kungiyar Mansfield bayan da Luis Suarez ya ciwa Liverpool din kwallonta ta biyu da ake ganin ya taba da hannu kafin ya ci a karawar da kungiyoyin biyu suka yi a zagaye na uku na gasar cin Kofin Kalubale na Ingila.

Daniel Sturridge ne wanda wasansa na farko ke nan da ya fara bugawa Liverpool ya jefa kwallon farko a minti bakwai da fara wasan.

Duk da cewa Liverpool ce ke kan gaba da kwallo daya amma Mansfield ce ke wasa sosai kafin Suarez da ya shigo daga baya ya jefawa Liverpool din kwallonta ta biyu wadda ake ganin ya taba da hannu kafin ya saka ta a raga.

Matt Green ya ramawa Mansfield kwallo daya a minti na 79, duk da kokarin da suaka yi ta yi basu sami damar rama ta biyu ba.

Da wannan nasara Liverpool ta sami damar zuwa zagaye na hudu na gasar Kofin Kalubalen.

Karin bayani