Kocin Najeriya ya sallami 'yan wasa

rabiu, ibrahim
Image caption Rabiu Ibrahim ba zai je Afrika ta Kudu ba

Kocin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya Stephen Keshi ya sallami wadansu 'yan wasa daga cikin jerin 'yan wasan kasar na wucin gadi na gasar Kofin Kasashen Afrika.

'yan wasan da kocin ya sallama daga sansaninsu na horo a Portugal sun hada da Rabi'u Ibrahim na kungiyar Kilmarnock da Papa Idris na Kano Pillars da Henry Uche na Enyimba da kuma Uche Kalu dake wasa a kasar Turkiyya wanda ya ji rauni.

Tuni daman Keshin ya fidda rai da samun Danny shittu na Millwall da Shola Ameobi na Newcastle United domin zuwa gasar ta Kofin Afrika.

Rabi'u Ibrahim dai ya rasa gurbi a jerin 'yan wasan ne saboda rashin zuwa sansanin horon na Portugal a kan lokaci da kuma rashin bugawa tsohuwar kungiyarsa ta Celtic wasanni.

A makon da ya wuce ne dan wasan mai shekaru 21 ya bar kungiyar Celtic ya koma Kilmarnock sabo da rashin samun damar bugawa kungiyar wasa a-kai-a-kai.

Dan wasan yana daga cikin 'yan wasan Najeriyar 'yan kasa da shekaru 17 da suka dauki Kofin Duniya a Korea a 2007.

A da ana ganin shi ne zai gaji Jay-Jay Okocha wajen bugawa kasar wasa a tsakiya abin da kasar ta rasa na wani gwanin da zai cike gurbin na Okocha cikin shekarun nan.

A ranar Talatar nan kocin na Najeriya, Stephen Keshi zai fidda jerin sunayen 'yan wasan da zasu yiwa kasar wasan gasar Kofin Afrikan , rana daya kafin wa'adin mika sunayen 'yan wasan gasar.

Karin bayani