Messi ya sake zama gwarzon duniya

lionel messi
Image caption Lionel Messi ya sake zama gwarzon duniya na 2012

Lionel Messi ya sake zama gwarzon dan kwallon duniya na Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA na shekara ta 2012.

Wannan shi ne karo na 4 da Messin dan kasar Argentina kuma dan kungiyar Barcelona ya ke samun kyautar a jere.

A bikin da aka yi a hedikwatar hukumar ta FIFA dake Zurich Messi ya sami galaba ne a kan Cristiano Ronaldo dan Portugal da kungiyar Real Madrid da kuma Andres Iniesta na Spain da kuma klub din Barcelona.

Karin bayani