Takaitaccen tarihin kwallon Ghana

Takaitaccen tarihin kwallon Ghana
Image caption Tawagar Ghana na da kwararrun 'yan wasa

Ghana ta kasance daya daga cikin kasashen Afrika da ake saran za su taka rawar gani a gasar da za ayi a Afrika ta Kudu.

Tawagar Black stars ta kasar Ghana dai ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya da aka yi a shekara ta 2010, inda ta zamo kasar Afrika daya tilo da ta tsallake zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe.

Ta sha kashi ne a hannun Uruguay a bugun fanareti.

Karfin tawagar Black stars dai ya ragu ganin cewar shahararren dan wasanta da ke taka leda a Real Madrid Micheal Essien ba zai taka mata leda ba.

Sannan kuma kocin kasar ya ajiye Andrew Dede Ayew wanda ke taka leda a kulob din Marseille na kasar Faransa.

A yanzu Kociya Kwesi Appiah zai dogara ne kan Kwadwo Asamoah na Juventus da Sulley Muntari da Asamoah Gyan da kuma Ricahrd Gkingston.

Kalubalen da ke gaban kocin dai shi ne ya kai matakin akalla zagayen kusa da na karshe a Afrika ta Kudu.

Ghana na rukunin B inda za ta kara da kasashen Mali da Niger da kuma DR Congo.

Karin bayani