Guardiola zai koma horar da 'yan wasa

Pep Guardiola
Image caption Pep Guardiola na zaune ne a New York tun lokacin da ya bar Spain, amma yana bin wasannin da Barcelona ke yi

Tsohon manajan kulob din Barcelona, Pep Guardiola ya ce a shirye yake ya koma fagen horar da 'yan wasa, kodayake bai sanar da kulob din da zai koma ba.

Guardiola ya shafe watanni bakwai yana hutun kauracewa harkar wasan kwallon kafa.

Pep mai shekaru 41, wanda ya jagoranci Barca ta dauki kofuna 14 a kakar wasanni hudu, yanzu yana neman wani aiki.

Guardiola ya ce "Na yanke shawarar komawa horar da 'yan wasa, amma iya shawarar da na yanke kenan."

"Bani da wani kulob a raina, amma ina son komawa fagen horar da 'yan wasa." Inji Pep

An yi ta rade-radin inda zai koma, tun bayan lokacin da ya bar mukaminsa a kulob din Barcelona.

Manajan Manchester United, Sir Alex Ferguson ya sanar da tsohon dan wasan tsakiyar Spaniya, a matsayin daya daga cikin wadanda yake ganin za su iya maye gurbinsa.

Yayin da kuma wasu ke cewa zai koma Chelsea.

Haka kuma an ce tsohon gwarzon mai horar da 'yan wasan na duniyan zai koma Bayern Munich.