Tarihin John Obi Mikel

Mikel Obi
Image caption Mikel Obi yana haskakawa sosai a Chelsea

An haifi Mikel Obi a garin Jos dake Najeriya, kuma cikakken sunansa shi ne John Michael Nchekwube Obinna. Da ne ga Michael Obi wanda ke da kamfanin sufurin motoci a Jos babban birnin jihar Plato.

Ya fara wasan kwallo yana da shekaru 12, a lokacin da aka gano yana da baiwa a wani gwajin basira da makarantar kwallon kafa ta kamfanin Pepsi ya shirya, wanda ya hada matasa 3000.

A wancan lokaci tawagar na zagawa fadin kasar du zummar zakulo masu baiwa, wadanda a nan gaba za su iya buga wasan kwallo a matsayin kwararru.

Bayan zakulo Mikel ya yi wasa a kungiyar kwallon kafa ta jihar Plato, wacce ta samar da wasu kwararrun 'yan wasa kamar Celestine Babayaro da Victor Obinna da Chris Obodo da sauransu.

Wadanda dukkaninsu sun koma bugawa kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai wasa.

Taka rawa a Najeriya

John Obi Mikel ya fara suna a lokacin da ya bugawa kungiyar kwallon kasar 'yan kasa da shekaru 17 wasa a Finland.

Daga bisani ya je gwaji kulob din Ajax dake Cape Town a Afrika ta Kudu wasa, kafin ya koma kulob din Lyn na Norway.

A ranar 12 ga watan Satumbar, 2006 ne kuma Mikel ya fara wasa da kulob din Chelsea a gasar UEFA, a lokacin da suka saye shi a wani yanayi mai cike da rudu daga kulob din Lyn Oslo na Norway. Hukumar kula da kwallon kafa ta tuhumi Mikel da rashin da a ranar 22 ga watan Nuwambar 2012.

Hakan ya sa aka hana shi buga wasanni uku kuma aka ci shi tararsa fam dubu 60, saboda barazanar da ya yi wa alkalin wasa, Mark Clattenburg a wasan da Celsea ta sha kaye a hannun Manchester United da ci 3-2.

Mikel ya fara wasan farko a kungiyar kwallon kafa ta kasa a ranar 17 ga watan Agustan 2005, a lokacin da aka yi musayarsa bayan hutun rabin lokaci a wasan sa da zumunci da Libya.

Daga nan bai kara bugawa kasar wasa ba, gabbannin bayyana sunansa cikin tawagar Najeriya da suka buga wasa a gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2006.

Kafin fara wasanninsu na League a shekara ta 2012, an sace mahaifin Mikel Obi a Najeriya a ranar 10 ga watan Agusta, kodayake hakan bai hana shi taka leda a karawar kulob dinsa da Stoke City ba.

Karin bayani