Najeriya ta kyale Ameobi da Shitu

shola ameobi
Image caption Shola Ameobi ya tsallake hukuncin Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ce ba zata hukunta Shola Ameobi da Danny Shitu ba a kan kin amsa gayyatar da suka yi ta zuwa gasar cin kofin Afrika.

Da farko an sanya sunayen 'yan wasan cikin jerin 'yan wasa 32 na wucin gadi, amma Ameobi dake bugawa kungiyar Newcastle ya yi watsi da goron

gayyatar shi kuwa Shittu ya roki kasar ta yafe masa zuwan.

A kan hakan Hukumar Kwallon ta Najeriya a da ta ce za ta nemi takwararta ta Duniya , FIFA, ta hukunta kungiyoyin 'yan wasan biyu idan ba su bari

sun amsa gayyatar ba.

Wani daga cikin 'yan hukumar gudanarwar Hukumar Kwallon kafar ta Najeria Chris Green ya ce a yanzu sun sauya shawara tun da dai suna da wasu

kwararrun 'yan wasan gara su maida hankali a kansu kada su raba hankalinsu.

A ranar Talatan nan ne dai kocin Najeriyar Stephen Keshi, zai bayyana sunayen 'yan wasa 23 da zai tafi da su gasar kamar yadda aka tsara a da

amma yanzu sai ranar Laraba rana ta karshe ta wa'adin mika jerin sunayen 'yan wasan.

Jami'in hukumar wasan ta Najeriya ya ce sun yi hakan ne domin hukumar ta yiwa jerin sunayen karatun ta natsu kafin a mika don gudun kada a

sami wata matsal daga baya, amma ba wai yin katsalandan ga shirin kocin ba.

Najeriya wadda ke rukuni na uku Group C, za ta fara karawa ne da Burkina Faso ranar 21 ga watan nan na Janairu sannan ta yi da Zambia masu rike da Kofi da kuma Habasha daga bisani.

Karin bayani