Adebayor zai buga wa Togo wasa

Emmanuel Adebayor
Image caption Emmanuel adebayor ya zura wa Tottenham kwallye uku a fita 17 a kakar wasannin da ake ciki

Kulob din Tottenham ya amince dan wasan nan Emmanuel Adebayor ya buga wa kasar Togo wasa a gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Tafiyar dan wasan ya bar kulob din da dan wasan gaba daya kacal da ya yi suna wato Jermain Defoe.

Da fari dai Adebayor mai shekaru 28 bai yi niyyar barin kulob din ba, saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da kungiyar kwallon kafa ta Togo, a kan batun tsaro na 'yan wasa da kuma kudaden alawus.

Sai dai a yanzu zai tafi kasar Afrika ta Kudu domin shiga gasar da za a fara a ranar 19 ga watan Janairun da muke ciki.

Adebayor ba zai samu buga wasanni shida tare da kulob din na Tottenham ba.

Haka kuma babu cikakken bayani game da ko zai samu shiga taka ledar da Spurs za ta yi da QPR a ranar Asabar.

Tuni dai Adebayor ya isa Ghana inda sauran tawagar Togo ke horo, amma Tottenham na fatan zai iya komawa domin buga wasan, sannan daga bisani ya koma.

Bayan karawarsu da QPR, Tottenham za ta dauki bakuncin Manchester United a ranar 20 ga watan Janairu, kafin kulob din ya nufi Leeds ko Birmingham domin gasar cin kofin kalubale na ingila wato FA, a ranar 26 ga wannan wata.

Bayan tafiyar Adebayor, nauyin zura wa Spurs kwallo ya fada kan Defoe, wanda ya zura kwallaye 14 a fita 28 da ya yi a kakar wasannin da ake ciki.