Mali ta rasa wasu fitattun 'yan wasa

dan wasan Mali
Image caption Mali ta rasa 'yan wasa zuwa gasar kofin Afrika

Kasar Mali ta rasa wasu fitattun 'yan wasanta hudu zuwa gasar cin kofin Afrika sakamakon raunuka da kowannen su ke fama da shi.

Tsohon kyaftin din kasar Mahamadou Diarra wanda ke cikin tawagar 'yan wasan yanzu ya ra damar zuwa gasar saboda rauni.

Haka kuma kociyan kasar ta Mali Partrice Carteron ya cire sunan Abdou Tarore da Mustapha Yatabare da ke wasa a Faransa da kuma Tongo Doumbia na kungiyar Wolverhampton wadan da dukkannin su 'yan wasa ne da ke bugawa kasar wasa akai-akai.

Duka 'yan wasan ba su sami damar shiga shirye-shiryen tawagar 'yan wasan kasar na makon karshe na zuwa gasar ba a Bamako babban birnin Malin.

Da alamu kuma dan wasan gasar Serie A ta Italiya Mamadou Samassa ya tsallake rijiya da baya wajen zuwa gasar domin duk da raunin da ya ji ana saran zai iya warke wa har ya buga wasan farko da Malin za ta yi da Nijar ranar 20 ga watan Janairun nan.

Wannan na nufin Mana Dembele haifaffen Faransa ba zai sami gurbin zuwa gasar ba, bayan da aka gayyato shi atisaye a karshen makon da ya wuce domin maye gurbin Samassan.

Rashin zuwan tsohon kyaftin din na Mali wanda ya ji rauni a wasansu da Botswana na neman cancantar zuwa gasar na nufin cewa gwanin dan wasan na kungiyar Fulham ba zai sami zuwa gasar ba sau biyu a jere, bayan da ya sami halartar na baya har sau hudu..

Shi kuwa Momo Sissoko dan wasan Paris St Germaine ya sami shiga cikin jerin 'yan wasan na Mali duk da cewa ba ya bugawa kungiyarsa wasanni sosai a bana kuma rabonsa da bugawa Malin wasa tun 2010 a gasar cin Kofin Afrika a Angola.

Karin bayani