Tawagar Najeriya ta kunshi 'yan kwallon gida

Joseph Yobo
Image caption Joseph Yobo shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da za su Afrika ta Kudu

Najeriya ta dauki 'yan wasa shida dake wasa a cikin gida, a jerin sunayen 'yan wasa 23 da ke tawagar kasar, da za su je Africa ta Kudu.

Kasar dai ta kwashe sama da shekaru ashirin rabonta da ta sanya 'yan wasan cikin gida a tawagar gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Mai horar da 'yan wasan, Stephen Keshi ya ce " sun cancanci shiga, kuma ina ganin wannan tamkar wata dama ce da 'yan wasan cikin gidan zasu nuna cewa, ba a yi zaben tumun dare ba."

"Na yi amanna da 'yan wasan da na zaba." In ji Keshi

Ya kara da cewa "An dora musu wani nauyi ne, kuma ina da tabbacin ba za su ba mu kunya ba. "

An dai cire sunanyen dan wasan gaba dake zaune a Amurka, Bright Dike da kuma dan wasan tsakiya Raheem Lawal wanda ke wasa a Turkiyya, a tawagar Najeriyar.

Jerin 'yan wasan

Masu tsaron gida: Vincent Enyeama (Maccabi Tel Aviv, Israel), Austin Ejide (Hapoel Be'er Sheva, Israel), Chigozie Agbim (Enugu Rangers)

'Yan baya: Elderson Echiejile (SC Braga, Portugal), Juwon Oshaniwa (Ashdod FC, Israel), Joseph Yobo (Fenerbahce, Turkey), Efe Ambrose (Celtic, Scotland), Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves), Kenneth Omeruo (ADO Den Haag, Netherlands), Godfrey Oboabona (Sunshine Stars)

'Yan wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea, England), Nosa Igiebor (Real Betis, Spain), Ogenyi Onazi (|Lazio, Italy), Obiora Nwankwo (Padova, Italy), Fegor Ogude (Valerenga, Norway), Gabriel Reuben (Kano Pillars)

'Yan gaba: Ahmed Musa ( CSKA Moscow, Russia), Emmanuel Emenike (Spartak Moscow, Russia), Victor Moses (Chelsea, England), Sunday Mba (Enugu Rangers), Ikechukwu Uche (Villarreal, Spain), Brown Ideye (Dynamo Kiev, Ukraine), Ejike Uzoenyi (Enugu Rangers)