Manchester City ta ci Arsenal 2-0

'yan wasan Man City da Arsenal
Image caption Manchester City ta baiwa Arsenal kunya a gida

A cigaba da wasannin gasar Premier Manchester City ta tashi da Arsenal da ci 2-0 a gidan Arsenal, Emirates Stadium.

Milner ne ya ciwa City din kwallonta ta farko a minti na 21 da fara wasan, sannan kuma Dzeko ya kara ta biyu a minti na 32.

Yanzu Manchester City tana da maki 48 a bayan Manchester United ta daya a tebur da maki 55 a wasanni 22.

Arsenal kuwa ta cigaba da kasancewa da maki 34 amma da wasanni 21

Dukkanin kungiyoyin biyu sun kammala wasan da 'yan wasa goma goma bayan an kori Laurent Koscienlny na Arsenal a minti goma da wasa bayan da ya yi wa Edin Dzeko keta, shi ma kyaftin din City Vincen Kompany ya sami jan kati a kusan karshen wasan saboda laifin keta.

Wannan shi ne karon farko da Man City ta sami nasara a kan Arsenal a gasar Premier a shekaru 38.

Wannan dai shi ne wasa na sati na 22 na gasar Premier ta Ingila.