Redknapp na neman 'yan wasa uku

harry redknapp
Image caption Harry Redknap na sha'awar Odemwingie

Kocin QPR Harry Redknapp na son sayen dan wasan West Brom Peter Odemwingie da kuma karbar aron Jake Livermore na Tottenham.

Redknapp ya bayyana hakan ne bayan wasansu da tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham wadda suka tashi 0-0, inda ya ce sun gudanar da bincike a kan dan wasan.

Kocin ya ce bai sani ba ko babban jami'in klub din nasu Philip Beard ya mika takardar bukatar sayen dan wasan amma yace dan wasa ne da suka yi magana a kansa da kuma yake neman sa.

Amma dai ya ce yana kyautata zaton cewa kungiyar tasu ta mika bukatar sayen dan wasan.

Odemwingie mai shekara 31 bai buga wasan da West Brom ta yi da Reading wadda ke matakin faduwa daga gasar Premier tare da QPR ba ranar Asabar, wasan da West Brom din ta yi rashin nasara.

Game da Livermore dan shekara 23 na kungiyar Tottenham kuwa, Redknapp ya ce zai dauke shi a matsayin aro.

Sai dai kuma kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya nuna alamun cewa ba zasu bada aron dan wasan ko kulla wata yarjejeniya a kansa ba.

Haka kuma kocin na QPR yana sha'awar sayen dan wasan Rennes M'Vila, wanda ya ce ya yi kokarin ya saye shi lokacin yana kocin Tottenham kuma ya kalli wasansa sau biyar ko shida a bara, sai dai kuma ya ce abu ne mai wuyar gaske ka jawo hankalin 'yan wasa idan kana baya a gasar da kake ciki wato kasan tebur.