An bude gasar Tennis ta Australia Open

Venus Willaims
Image caption Venus Willaims

A yau ne aka bude gasar Tennis na Australia Open na shekarar 2013 a Birnin Melbourne, wanda ake yi duk shekara.

Inda 'yan wasa Maria Sharapova da Venus Willaims suka doke abokan karawarsu.

Haka kuma dan wasa, Novak Djokovic na cikin wadanda suka samu nasara, a wasannin da aka yi da safiyar yau a gasar.

Ita kuwa 'yar Birtaniya Heather Watson ta samu zuwa zagaye na biyu, bayan doke Alexandra Cadantu.

Yayin da Lleyton Hewitt zai fafata da Janko Tipsarevic.