An soke hukuncin Kompany

Vincent Kompany
Image caption Vincent Kompany ya tsallake hukunci zai cigaba da buga wasa

Kungiyar Manchester City ta yi nasara a daukaka karar da ta yi ta hukuncin da alkalin wasa ya yi na korar kyaftin din ta Vincent Kompany a wasan kungiyar da Arsenal.

Hukumar kwallon Kafa ta Ingila ce ta soke hukuncin, wanda a da ya haramtawa dan wasan buga wasanni uku.

Hukumar ta ce ta amince da korafin kungiyar ta Manchester City na kuskuren hukuncin korar dan wasan a karawar ta ranar Lahadi.

Manchester City ta shigar da kara ne a kan cewa alkalin wasan ya yi kuskure a hukuncin domin yadda Kompany ya kalubalanci Wilshere din ba mugunta ba ce.

Alkalin wasa Mike Dean ya kori Kompany saboda keta da ya ke ganin dan wasan ya yi wa Jack Wilshere na Arsenal a wasan da manchester City ta yi nasara 2-0.

Karin bayani