Serena, Federer, Azarenka sun yi nasara

serens williams
Image caption Serena Williams ta yi nasara a Australian Open

A rana ta biyu ta gasar wasan Tennis ta Australian Open Roger Federer zakaran gasar sau hudu da Victoria

Azarenka mace ta daya a duniya a wasan na tennis da Serena Williams wadda sau biyar tana daukar kofin gasar

dukkanninsu sun yi nasara a Melbourne.

Haka su ma 'yan Birtaniya Andy Murray da Laura Robson sun sami nasarar zuwa zagaye na biyu sai dai Jamie

Baker shi ma na Birtaniyan ya yi rashin nasara, an fidda shi daga gasar.

Sakamako

Andy Murray na uku a duniya ya yi nasara ne a kan Robin Haase dan kasar Netherlands da ci 6-3 6-1 6-3.

Victoria Azarenka 'yar Belarus ta yi galaba a kan Monica Niculescu 'yar Romania da ci 6-1 6-4.

Shi kuwa Roger Federer na biyu a duniya dan Switzerland ya buge Benoit Paire dan Faransa ne da ci 6-4 6-2 6-1.

Serena Williams 'yar Amurka ta uku a duniya ta yi galaba a kan Edina Gallovits-Hall 'yar Romania da ci 6-0 6-0.

Laura Robson ta yi nasara a kan Melanie Oudin 'yar Amurka da 6-2 6-3.

Jamie Baker ya yi rashin nasara a hannun Lukas Rosol dan Czech da ci 7-6 (7-5) 7-5 6-2.

Jo-Wilfried Tsonga na Faransa na bakwai a duniya ya yi nasara a kan Micheal Llodra shi ma dan Faransa da ci 6-4 7-5 6-2.

Juan Martin Del Potro na Argentina na shida a duniya ya buge Adrian Mannarino dan Faransa da ci 6-1 6-1 6-2.