'Yan Ethiopia za su sha kudi

filin gasar kofin afrika
Image caption 'Yan wasan Ethiopia za su sami makudan kudade idan su ka dau kofi

'yan wasan kwallon kafa na Ethiopia wato Habasha za su sami dalar Amurka dubu 111 kowannensu idan su ka yi nasarar daukar kofin Afrika.

Shugaban Hukumar Kwallon kasar Sahilu Gebremariam ya ce za a baiwa kowana dan wasa wannan kudi idan su ka

dauki kofin kuma za a ba kowa dala dubu 55 ta kaiwa zuwa gasar.

Kasar wadda zata baiwa 'yan wasan wadannan makudan kudade bayan talaucin da ta ke fama da shi ta sami

nasarar sake dawo wa gasar ne bayan shekaru talatin ana yi ba ita.

Mr Sahilu ya ce kocin kungiyar Sewnet Bishaw da mataimakin sa za su sami adadin da ya zarta na 'yan wasan idan

kasar ta kai ga wasan karshe.

Ethiopian ta sami nasarar daukar kofin na Afrika a 1962, tun daga nan kuma ba ta kara samun nasarar zuwa gasar

ba sai a 1982.

An hada ta da kasashen Najeriya da Zambia da Burkina Faso a rukuni na uku, wato Group C, kuma ana ganin da

wuya ta iya fitowa daga rukunin.

Sai dai kocinsu Mr Sewnet ya ce ''wasan kwallon kafa ne, komai na iya faruwa, na mamaki.

Ya ce ''ko da ike dai sabon wuri ne ga 'yan wasan amma sun taka rawar gani sosai a manyan wasanni a

kwanannan.

Kocin ya ce an yi musu alkawarin kudaden ne domin karfafa mu su guiwa.

Ya ce ya tabbata cewa sauran jama'a 'yan kasuwa da fitattun mutane za su kara mu su wasu kyaututtkan ma idan

su ka sa kasar alfahari a Afrika ta Kudu.

A karshen makon da ya wu ce ma hamshakin attajirin nan dan kasar Saudi Arabia haifaffen Habashan Sheik

Mohammed Al Amoudi ya baiwa kowana dan wasa a tawagar kasar dala dubu 11 saboda nasarar zuwa gasar ta

Kofin Afrikan.

Kocin ya ce 'yan wasan sun sani cewa zasu sami fiye da haka idan su ka dauki kofin.