QPR ta sayi Loic Remy na Marseille

loic remy
Image caption Loic Remy ya ce lokaci ya yi da zai koma gasar premier

Kungiyar Queens Park Rangers ta dauki dan wasan kungiyar Marseille ta Faransa Loic Remy a kan fam miliyan 8.

Remy mai shekara 26 ya amince da yarjejeniyar shekara hudu da rabi a kungiyar ta karshe a gasar Premier.

Tsohon dan wasan na Lyon ya bugawa Faransa wasa sau 17 kuma ya ci kwallaye 4.

Harry Redknapp ya ce ya yi matukar farin ciki da kawo dan wasan wanda zai iya zama fitaccen gwani a nan gaba.

Kungiyar Newcastle ma ta yi harin sayen shi kuma ta na saran tattaunawa da shi ranar Lahadi sai kawai ta sami labarin ya tafi QPR din.

Redknapp ya ce ''dan wasa ne da na dade ina sha'awa, na kalli wasan sa a lokuta da dama gaba dayan shekarar da ta wuce, na gana da shi tsawon sa'oi 3 ko 4 a bara don haka ya san yadda na dauke shi kuma hakan na da muhimmanci.

Remy wanda ya ci wa Marseille kwallaye uku a wasanni 19 a bana ya ce Harry ya taka rawa sosai wajen zuwan sa klub din na QPR.

Dan wasan ya ce bayan shekaru 7 a Faransa wannan lokaci ne da ya dace ya fuskanci wani kalubalen a gasar Premier, gasar da ta fi kowace gasa a duniya, in ji shi.

Karin bayani