Robson ta fitar da Kvitova

laura robson
Image caption Laura Robson ta shiga zagaye na uku na Australian Open

Laura Robson ta sami nasara a kan tsohuwar tauraruwar Wimbledon Petra Kvitova a gasar tennis ta Australian Open.

Laura wadda ita ce ta biyu a mata gwanayen wasan tennis a Birtaniya ta sami galaba ne a kan Kvitova 'yar kasar

Czech wadda ita kuma ta ke matsayi na takwas a kasarta da ci 2-6 6-3 11-9.

Robson wadda za ta cika shekara 19 ranar Litinin ta farfado ne a zagaye na karshe lokacin takwarar tata ta na

gabanta da maki 3 ba ko daya ta sami nasara inda ta bi sahun 'yar uwarta ta Birtaniya Heather Watson zuwa zagaye

na uku na gasar.

A gaba za ta kara ne da Sloane Stephens ta 29 a gwanayen tennis mata a Amurka, kuma ana ganin ta na da damar

maimaita bajintarta ta gasar US Open inda ta yi nasara a kan Li Na 'yar China da Kim Clijsters ta Belgium kan

hanyarta ta zuwa zagayen 'yan 16.

Karin bayani