Galibin 'yan wasan Afrika a Turai su ke

'yan wasan africa
Image caption 'yan wasa 188 daga 368 na gasar Afrika daga Turai su ke

Wani bincike na Gamayyar Kungiyoyin Wasan Kwallon Kafa na Kasashen Turai (ECA), ya nuna cewa sama da rabin 'yan wasan gasar Kofin Afrika da za a yi a Afrika ta Kudu daga kungiyoyin Turai su ke.

Kungiyar ta ce kasar Ivory Coast ita ce da mafi yawan 'yan wasan inda 21 daga cikin 23 su ke wasa a Turai wadanda su ka hada da 'yan uwan nan Yaya da Kolo Toure daga Manchester City, Didier Drogba kuwa yana wasa ne a China.

Ethiopia kuwa ita ce da mafi yawan 'yan wasan da su ke wasa a gida su 20.

Kungiyar ta ECA ta ce 'yan wasa 188 daga cikin 368 da za su yi wasa a gasar Kofin Afrikan su na wasa a Turai, inda suke wakiltar kungiyoyi 137 daga gasar lig-lig 26 na Turai.

Kungiyoyi 55 na Faransa sun samar da 'yan wasa 55 da su ka hada da biyar-biyar daga kungiyoyin Ajaccio da Brest da Evian.

Guda ashirin kuma na kungiyoyin Ingila ne.

'Yan wasa 155 kuwa suna wasa ne a kungiyoyin Afrika, dan wasa daya na Ethiopia Fuad Ibrahim daga kungiyar Minnesota Stars dake Amurka ya ke.

Karin bayani