Suarez ya harzuka Rodgers

luis suarez
Image caption Luis Suarez ya ce da gan-gan ya fadi

Kocin Kungiyar Liverpool Brendan Rodgers ya ce ikirarin da dan wasansa Luis Suarez ya yi na cewa ya fadi da

gan-gan domin samun bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a wasansu da Stoke City a watan Oktoba ya bata masa rai.

Kocin ya ce kungiyar za ta hukunta dan wasan dan kasar Uruguay kan zambar.

Rodgers ya ce ''abu ne da bai dace ba kuma da ba za a amince da shi ba, na yi magana da Luis kuma za mu dauki mataki a kungiya.''

Dan wasan mai shekara 25 ya bayyana hakan ne a wata hira a shirin wasanni na talabijin na Fox Sports na Argentina.

Kocin Stoke City din Tony Pulis ya soki lamirin Suarez din bayan wasan.

Mataimakin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA Jim Boyce shi ma ya yi magana a kan lamarin inda ya ce

zambar faduwa da gan-gan a wasa cutar daji ce da take bata wasan.