Djokavic ya yi galaba a kan Wawrinka

novak djokovic
Image caption Novak Djokovic na kan hanyar kafa tarihi a Australian Open

Zakaran gasar tennis ta Australian Open Novak Djokavic ya sha da kyar a hannun Stanislas Wawrinka.

Djokavic ya yunkuro ne ya na bayan Wawrinka da maki 6-1 5-2 ya sami nasara 1-6 7-5 6-4 6-7 (5-7)12-10 a filin wasa na Rod Laver Arena.

Yanzu Djokavic zai hadu da Tomas Berdych a wasan gab-da-na-kusa-da-na-karshe.

Djokavic dan shekara 25 ya na kan hanyarsa ta zama mutum na farko da zai zama zakaran gasar ta Australian Open sau uku a jere tun lokacin da aka fara ta a 1968.