Ghana da DR Congo sun tashi 2-2

'yan wasan dr congo da ghana
Image caption Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ta hana Ghana nasara

Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ta hana Ghana samun nasara a wasan farko na rukuni na biyu wato Group B a gasar Kofin Afrika bayan da ta rama kwallaye biyun da Ghanan ta fara ci.

Ghana ta jefa kwallon farko ta gasar a minti na 40 lokacin da Emmanuel Agyemang Badu ya yi amfani da damar da ya samu ta kwallon da Kwadwo Asamoah ya bashi.

A minti na 49 ne kuma Asamoah ya sake jefa wa Ghana kwallonta ta biyu da ka.

Minti hudu tsakani ne Tresor Mputu ya jefa wa Jamhuriyar Congo kwallonta ta farko.

Congon ta rama kwallo ta biyu a minti na 69 ta hannun Dieumerci Mbokani a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida bayan da aka ja rigarshi ya fadi.

Karin bayani