Mali ta ci Niger 1-0 a gasar Afrika

'yan wasan mali da niger
Image caption Mali ta zama ta farko da ta sami nasara a gasar Kofin Afrika

Kasar Mali ta zama ta farko da ta sami nasara a gasar cin Kofin Afrika ta 2013 wadda ake yi a Afrika ta kudu.

Malin ta samu nasara ne a kan Jamhuriyar Nijar da ci 1-0, ta hannun kyaftin dinta Seydou Keita.

Saura minti 6 a tashi daga wasan wanda ake ganin za a tashi canjaras ba bu ci sai tsohon dan wasan Barcelonan ya ci kwallon.

Mai tsaron gidan Nijar Daouda Kassaly ne ya kasa kama kwallon da Fousseiny Diawara na Mali ya bugo daga gefe wanda hakan ya baiwa Keita damar jefa kwallon a raga.

Wannan nasara ta baiwa Mali damar zama ta daya a rukuni na biyu wato Group B bayan Ghana da Jamhuriyar Dumokradiyya Congo sun tashi 2-2.