Tottenham da Man U sun yi 1-1

robin van persie
Image caption Robin Van Persie ya ci kwallonsa ta 22

Dan wasan Tottenham Clint Dempsey ya ciwa kungiyarsa kwallo a dai-dai minti na 93 a karawarsu da Manchester United.

Har a minti na 92 bayan kara mintina 5 a karshen minti na 90 na ka'ida Manchester United na sa ran tsira da nasara amma ta rasa wannan dama a minti na 93.

A minti na 25 ne Robin Van Persie ya jefa wa Manchester United kwallonta ta farko, wadda ita ce kwallo ta 22 da ya ci a kakar wasanni ta bana.

Da wannan sakamako na 1-1 tsakanin Tottenham din da Manchester United, yanzu ya rage maki 5 kawai tsakanin United ta daya a Premier da Manchester City.

Manchester United ta saba cin kwallo a kusan karshen lokaci amma a wannan karon ita aka ci da hakan.