Benitez ya kare Torres

rafeal benitez
Image caption Rafeal Benitez ya ce Torres ya na kokari sosai

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Rafeal Benitez ya ce mutanen da su ke sukan Fernando Torres ta amfani da kididdiga ba su da wata masaniya.

Benitez ya ce idan ka na da dan wasan gaba daya da ka ke amfani da shi tsawon wata daya da rabi ba ka sauya shi ba abu ne mai wuyar gaske ga dan wasan.

Amma yanzu tun da ka na da 'yan wasan gaba biyu za ka iya amfani da su a lokuta daban daban.

Kocin ya ce ''Fernando ya na kokari sosai, sannan kuma yanzu ga Demba Ba ya na bamu abinda da ba mu da shi.''

Wasanni bakwai ne zuwa lokacin karawar Chelsea da Arsenal Torres dan kasar Spain mai shekaru 28 bai ci kwallo ba.

A wasan Chelsea da Southampton da su ka ta shi 2-2 magoya bayan Chelsea sun rika yi wa Torres eho.

Tun shekaru biyu da Chelsea ta sayi dan wasan daga Liverpool a kan fam miliyan 50 kwallaye 14 a wasannin Premier 69 kawai ya ci.

Karin bayani