Gasar da ba Brazil ko Argentina

dan wasan argentina
Image caption 'Yan Argentina sun gamu da koma baya tun 2007

Nan da 'yan watanni za a samu sabon tarihi a wasan kwallon kafa inda za a yi gasar 'yan kasa da shekara 20 ta duniya ba tare da Brazil ko Argentina ba.

Wannan ne karon farko da za a yi gasar kofin kwallon kafa ta matasa ta duniya ba bu Brazil ko Argentina.

Ba bu daya daga cikin Kasashen biyu da ta samu cancantar zuwa gasar ta duniya da za a yi a Turkiyya.

Manyan kasashen a fagen kwallon kafa na duniya ba su fito daga wasannin neman cancantar ba na yankin Latin Amurka.

'Yan wasan Brazil da su ne zakarun duniya a matakin 'yan kasa da shekaru 20 din sun kasance na karshe a rukuninsu na kasashe 5, ko da zagaye na biyu ba su fito ba.

Haka ita ma Argentina ta kammala wasan rukuninta ne a matsayin ta kusa da ta karshe.

Sau biyar Argentina ta na daukar kofin matasan 'yan kasa da shekara 20 tsakanin 1995 da 2007.

Tun daga wannan lokacin ne kuma kasar ta rika samun koma baya a bangaren wasanninta na matasa.

Karin bayani