Murray ya kai wasan dab da kusa da na karshe

Image caption Andy Murray ya doke Gilles Simon

Andy Murray ya kai wasan dab da kusa da na karshe cikin sauki bayan ya doke Gilles Simon a gasar Austrailian Open.

Murray ya yi nasara ne da maki 6-3 6-1 6-3 a wasan da aka buga cikin sa'a guda da mintuna 32.

Murray, mai shekaru 25, ya kai wasan dab da kusa da na karshe a shekaru hudu a jere kuma kuma zai fafata ne da Jeremy Chardy a ranar Laraba.