NFF ta gargadi Stephen Keshi

Stephen Keshi
Image caption Keshi ya samu goyon bayan 'yan Najeriya lokacin da aka nada shi

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta gayyaci kocin Super Eagles, Stephen Keshi saboda wasan da Najeriya ta tashi kunen doki tsakaninta da Burkina Faso a wasan farko na gasar cin kofin kasashen Afrika.

Super Eagles ta zira kwallonta a minti na 23 inda Emmanuel Emenike ya ci kwallon amma kuma sai a cikin karin lokaci, Alain Traore ya farkewa Burkina Faso.

Shugaban NFF, Aminu Maigari ya shaida wa BBC cewar ya gayyaci Stephen Keshi da sauran masu horar da 'yan kwallon kasar don su yi bayani a kan abinda ya janyo kasar bata taka rawar gani ba.

"Kwamitin gudanarwa na NFF ya tattauna sannan ya gayyaci masu horadda 'yan kwallo, inda muka nuna musu fushinmu da takaici saboda kasa yin abinda aka za ta," kamar yadda Shugaban NFF Aminu Maigari ya shaida wa BBC.

"Mun nuna musu wasu 'yan kura-kuran da suke da su, da kuma rashin mayar da hankali don su yi gyara."

'Za su sauya'

A cewarsa, masu horar da 'yan kwallon sun dauki alkawarin zage damtse don a samu nasara a wasansu da Zambia da ke tafe.

"Sun dauki alkawarin cewar abubuwa za su sauya, sun ji dadin abinda muka nuna musu, inda suka ce za su yi duk mai yiwuwa a wasanmu da Zambia", a cewarsa.

Magoya bayan Super Eagles sun fice daga filin Mbombela a jiya da daddare cikin takaici saboda sun saran Keshi zai jagoranci kasar zuwa nasara.

Har yanzu Najeriya na kokarin lashe gasar kofin Afrika ne a karon farko tun bayan kofin da ta lashe a wasan karshen da ta doke Zambia a shekarar 1994.

Kuma a ranar Juma'a za ta sake fafata wa da Zambiar a gasar ta bana.

Ita ma dai Zambian wacce ita ce mai rike da kanbun gasar, ta tashi 1-1 ne a wasanta na farko da Ethiopia.

Karin bayani