Zambia da Ethiopia sun tashi 1-1

'yan wasan zambia da ethiopia
Image caption 'Yan wasan Zambia da Ethiopia sun yi canjaras

'yan wasan kwallon kafa na kasar Ethiopia wato Habasha sun tilastawa takwarorinsu na Zambia tashi 1-1 a karawar da suka yi ta gasar kofin Afrika.

Dan wasan Zambia, zakarun Afrika, Collins Mbesuma shi ya ci wa kasarsa kwallonta a minti na 45.

Adane Girma shi kuma ya ramawa Habasha kwallon a minti na 65 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

A farkon wasan Saladain Said na Habasha ya kasa cin bugun-daga-kai-sai-mai-tsaron-gida da kasar ta samu.

'yan Habashan su goma ne su ka karasa wasan bayan alkalin wasa ya kori maitsaron gidansu Jemal Tassew saboda keta da ya yi wa dan Zambia.

Dukkanin kasasshen biyu su na rukuni na uku ne wato Group C na gasar ta cin Kofin Afrika.

A daya wasan na rukunin na uku Najeriya ta na karawa da Burkina Faso.

Karin bayani