Bradford ta yi waje da Aston Villa

'yan wasan bradford
Image caption Bradford ta kafa tarihi a shekaru hamsin

Kungiyar Kwallon Kafa ta Bradford wadda ba ta kai rukunin gasar Premier ba ta zama ta farko daga wannan mataki a cikin shekaru hamsin da ta kai wasan karshe na Kofin Lig(Carling Cup) na Ingila.

Duk da galabar da Aston Villa wadda ke rukunin Premier ta samu a wasan da su ka yi karo na biyu da ci 2-1, 'yan Bradford din sun sami nasara da kwallaye 4-3 jumulla a wasan gida da waje.

Yanzu Aston Villa za ta yi wasan karshe tsakanin Chelsea da Swansea wadda ta yi nasara a tsakaninsu a karawar da za su yi.

A karawar Christian Benteke na AstonVilla mai masaukin baki shi ne ya fara jefa kwallo a ragar Bradford a minti na 24.

Sai dai a minti na 55 Bradford ta rama kwallon inda James Hanson ya ci da ka a farkon rabin lokaci.

Amma kuma ana dab da tashi daga wasan a minti na 89 Andreas Weimann na Aston Villa ya jefawa kungiyarsa kwallo ta biyu.

Karin bayani