Ferguson zai yi bayani game da zargin Beck

Sir Alex Ferguson
Image caption Hukumar ta taba neman Ferguson ya yi karin haske a lokacin da ya ce Alan Wiley bashi da koshin lafiyar da zaiyi alkalin wasa a karawarsu da Sunderland a 2009.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bukaci manajan kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya yi karin haske game da zargin mataimakin alkalin wasa.

Ferguson ya zargi Simon Beck da gaza baiwa Wayne Rooney damar buga fenariti.

Sir Alex ya yi zargin ne a lokacin karawarsu da kulob din Tottenham a ranar Lahadi, wasan da aka tashi kunnen doki.

Haka kuma manajan Man U din ya tado batun zura kwallon da dan wasan nan na Chelsea Didier Drogba ya yi a shekarar 2010.

Wanda shi ma a wancan lokaci Beck ne ya amince da zura kwallon, duk da cewa wasu na ganin Drogba ya keta ka'ida wajen zura kwallon.

Ferguson ya shaida wa BBC cewa "Ya bani haushi, dama ba tun yau ya fara yi mana irin haka ba."

Hukumar ta baiwa Ferguson nan da ranar Alhamis ya bayyana abin da yake nufi game da zargin da ya yiwa mataimakin alkalin wasan.