Ivory Coast ta ci Togo 2-1

dan wasan ivory coast
Image caption Ivor Coast ta soma gasar kofin Afrika da sa'a

Kasar Ivory Coast ta sami nasara a kan Togo da ci 2-1 a wasan rukuni na hudu wato Group D na cin kofin Afrika.

Yaya Toure ne ya fara jefa wa Ivory Coast kwallonta a raga a minti takwas da fara wasa.

A minti na arba'in da biyar kuma Togo ta rama kwallon ta hannun Ayite dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Ana dab da tashi ne kuma Gervinho ya ci wa Ivory Coast kwallonta ta biyu a minti na tamanin da takwas.

Da wannan nasara yanzu Ivory Coast ita ce ta daya a rukunin na hudu, Group D.

Karin bayani