Sharapova da Li Na za su kara

maria sharapova
Image caption Maria Sharapova ''ba na son in baiwa abokan karawata dama su jarraba ni''

Maria Sharapova ta ci gaba da bajintar da ta ke yi a inda ta sami nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar tennis ta Australian Open da galaba a kan 'yar kasarta Rasha, Ekaterina Makarova.

Da wannan nasara yanzu za ta fafata da Li Na 'yar China wadda ita kuma ta fitar da ta hudu a duniya Agnieszka Radwanska 'yar Poland daga gasar ta Australian Open.

Ita dai Sharapova ta biyu a duniya a jerin gwanayen tennis din mata 'yar Rasha ta yi narasa a kan Makarova ta 19 da maki 6-2 6-2.

Ita kuwa Li Na ta shida a duniya ta sami nasara ne a kan Radwanska ta hudu wadda wasanni 13 a jere ta ke samun nasara kafin Li ta fitar da ita a wannan karon da maki 7-5 6-3.

Karin bayani