Zaha: Man U za ta tattauana da Palace

Wilfried Zaha
Image caption Zaha shi ne matashin dan kwallon bara na gasar Premiership

Kulob din Manchester United da Crystal Palace za su tattauna don cimma yarjejeniya game da sayen dan wasan Ingila Wilfried Zaha.

Manajan Man U, Sir Alex Ferguson bai bi tawagar kulob dinsa zuwa Qatar, domin dan gajeren horo ba.

United na tayin sayen dan wasan gefen, a kan kudi fam miliyan 12, sannan kuma su ba da aronsa ga kulob din na Crystal a tsawon kakar wasannin da ake ciki.

Sai dai dukkanin kulob din biyu sunki cewa uffan, game da yarjejeniyar sayen dan wasan mai shekaru ashirin a duniya.

Amma ana sa ran za su cimma matsaya nan da karshen mako.