Michu ya saba kwantiragi da Swansea

michu
Image caption Michu '' ban taba jin dadin wasa ba kamar a Swansea''

Michu ya saba kwantiraginsa da Swansea City na wasu shekaru hudu har zuwa 2016.

Dan kasar Spaniya mai shekaru 26 Michu ya ce sabunta kwantiragin nasa mataki ne mai sauki a wurinsa saboda yana samun biyan bukatarsa a kungiyar.

Michu wanda ke iya wasa a tsakiya ko a gaba ya ci kwallaye 16 a wasanni 28 da ya buga wa Swansea City.

Dan wasan ya ce bai taba jin dadin wasansa ba kamar yanzu da yake klub din Swansea kuma yana alfahari da hakan shi yasa ma ya yanke shawarar ci gaba da zama a kungiyar.

Yace abu ne mai sauki wasa a kungiyar kuma ya sami damar zuwa wasan karshe a karon farko a rayuwarsa ta kwallon kafa; yana nufin wasan kusa da na karshe da Swansea za ta yi da Chelsea na Capital One Cup karawa ta biyu na ranar Laraba.

Karin bayani