Mourinho ya ce ba zai koma PSG ba

jose mourinho
Image caption Jose Mourinho ''ba na jin zan koma PSG''.

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya musanta rade-radin da ake yi cewa zai koma Kungiyar Paris St Germain ta Faransa domin maye gurbin Carlo Ancelotti.

Tsohon kocin na kungiyar Porto da Chelsea da kuma Inter Milan ya ce '' a'a bana jin zan koma PSG, nasarar da PSG ta samu da Ancelotti da Leornardo na nufin ba su da bukatar wani kocin''.

Ya kara da cewa '' ina yiwa Carlo da PSG fatan alheri''.

Mourinho ya ce ''Turai ta na bukatar birni kamar Paris da ya ke fafatawa a babban matakin kwallon kafa , kuma ina ganin wannan shiri yana tafiya dai-dai''.

PSG ta dauki Zlatan Ibrahimovic da Thiago Silva da kuma Ezequiel Lavezzi kuma ita ce ta daya a gasar Lig din Faransa a gaban Lyon amma da bambancin yawan kwallaye.

Karin bayani