Tennis: Stephens ta fitar da Serena

sloane stephens
Image caption Sloane Stephens na iya zama shahararriyar 'yar tennis a nan gaba.

Serena Williams wadda ake ganin za ta dauki kofin gasar tennis ta Australian Open ta fice daga gasar bayan da raunin da ta ke fama da shi ya hanata katabus a karawarta da Sloane Stephens a wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe.

Serena wadda sau 15 ta na daukar kofin babbar gasar tennis ta na gaban Stephens wadda ita ma ba Amurkiya ce a karawar tasu amma bayan da aka yi mata maganin ciwon bayan da ya ke damun ta a lokacin wasan sai matashiyar 'yar wasan ta wuce ta da maki 3-6 7-5 6-4.

An ji Serena 'yar shekara 31 a lokacin wasan tana kokawa da ciwon baya da kuma na diddige.

A ranar Alhamis ne Stephens 'yar shekara 19 za ta hadu da mai rike da kambun gasar ta Australian Open kuma ta daya a duniya Victoria Azarenka a wasan kusa da na karshe.

Haka kuma ta nuna irin gajiyar da ta yi saboda wasannin da ta fafata a cikin makwanni biyun da suka gabata.

Karin bayani