Swansea ta kafa tarihi da Chelsea

swansea da chelsea
Image caption swansea ta kafa tarihi na shekara dari daya

Kungiyar Swansea City ta samu nasarar zuwa wasan karshe na Kofin Lig na Ingila, Capital One, inda ta fitar da Chelsea da ci 2-0 jumulla a karawa biyu, gida da waje.

Wannan shi ne karon farko a cikin shekaru 100 na tarihin kungiyar ta Swansea da ta sami nasarar zuwa wasan karshe na wani babban kofin Ingila.

A wasan farko da aka yi makwanni biyu da suka wuce ne a gidan Chelsea Swansea ta ci kwallayenta biyu.

A karawar ta yanzu kuma a gidan Swansea an tashi ne ba ci.

A minti na tamanin alkalin wasa ya kori dan wasan Chelsea Eden Hazard saboda taka mai dauko kwallo a bayan fili da ya yi.

Da wannan nasara Swansea za ta yi wasan karshe da Kungiyar Bradford ranar 24 ga watan Fabrairu.

Karin bayani