Kofin FA - Leeds United 2 Tottenham 1

leeds tottenham
Image caption Leeds ta yi waje da Tottenham a gasar kofn kalubale na FA

Leeds United ta samu nasarar zuwa zagaye na biyar na gasar cin Kofin Kalubale na Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, bayan da ta ci Tottenham 2-1 a gida (Ellen Road).

Luke Varney shi ne ya fara ci wa Leeds kwallonta a minti na 15 da fara wasa bayan da 'yan wasan baya na Tottenham suka yi sakaci.

Dawo wa daga hutun rabin lokaci ke da wuya a minti na 51 sai Leeds ta kara kwallo ta biyu ta hannun Ross McCormack.

Minti bakwai daga wannan kwallo ne kuma sai bakin, 'yan Tottenham su ka sami damar saka kwallo daya wadda Clint Dempsey ya ci a minti na 58 da ka.