Djokovic ya yaba da nasararsa

novak djokovic
Image caption Novak Djokovic ''ina cin ganiyata ne yanzu kafin in ga abin da gobe za ta zo da shi ''

Zakaran wasan tennis na duniya Novak Djokovic ya bayyana nasarar da ya samu ta daukar kofin gasar Australian Open na hudu da cewa babban abun mamaki ne da kuma ban sha'awa.

Dan wasan dan kasar Serbia mai shekara 25 da ya buge Andy Murray na Burtania da maki 6-7 (2-7) 7-6 (7-3) 6-3 6-2 ya zama mutum na farko a shekaru 46 da ya yi nasarar daukar Kofin Gasar sau uku a jere a Melbourne.

Djokovic ya ce yana cike da farin ciki kuma nasarar za ta ba shi karfin guiwa a sauran lokacin kakar wasannin bana.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana ganin yana sauya yadda wasan tennis yake sai ya ce ''shekarata 25 kuma na dauki kofunan manyan wasanni guda 6 kuma ina da kofuna da yawa. Abun sha'awa ne.

Ina son in yi amfani da damar da na samu a yanzu in more ma ta matuka kuma in ga yadda gobe za ta kasance min''.

Sau uku ke nan Andy Murray yana shan kashi a wasan karshe na gasar ta Australian Open.

Karin bayani