Beckham ya yi atisaye da Arsenal

david beckham
Image caption David Beckham ba shi da kungiya yanzu

David Beckam ya yi atisaye da 'yan wasan Arsenal amma kuma kocin kungiyar Arsene Wenger ya kawar da maganar daukan tsohon kyaftin din na Ingila.

Beckam dan shekara 37 bai shiga wani klub ba tun lokacin da ya bar Los Angeles Galaxy a karshen kakar wasannin lig din Amurka.

Wenger ya ce tsohon dan wasan na Manchester United ya yi masa waya ne ya tambaye shi ko zai iya zuwa ya yi atisaye da 'yan wasan Arsenal din domin ya tsinka jininsa.

Sai dai kocin ya ce ba bu wani rade radin daukar dan wasan ko wani abu makamancin haka, da aka yi masa tambaya game da ko zai dauki dan wasan.

Tun farkon watan Disamba ne dai rabon Beckam da buga wasa lokacin da ya taimaka wa LA Galaxy ta cigaba da rike kofin gasar lig na Amurka da ta yi nasara da ci 3-1 a kan kungiyar Houston Dynamo.

Tun a lokacin ana danganta shi da tafiya kungiyoyin Paris Saint-Germaine da Monaco amma ya kafe cewa bai san inda zai nufa ba da wasa a gaba.

Sau 115 Beckam ya yi wa Ingila wasa kuma wasansa da kasar na karshe shi ne na lokacin neman cancantar shiga gasar Kofin Duniya da kasar Belarus a watan Oktoba na 2009.