An dakatar da Kocin Juventus

antonio conte
Image caption Antonio Conte ya soki alkalin wasa kan kin basu fanareti

An dakatar da kocin kungiyar Kwallon kafa ta Juventus ta Italiya Antonio Conte da wasu 'yan wasan klub din uku sabo da sukan lamirin alkalin wasa a wasansu na ranar Asabar da su ka yi 1-1 da Genoa.

'Yan wasan baya Leornardo Bonucci da Giorgio Chiellini da dan wasan gabaMirko Vucinic da jami'in kungiyar Giuseppe Marotta su ma na dakatar da su sabo da sukan alkalin wasan da suka yi saboda ya ki baiwa kungiyar bugun daga kai sai mai tsaron gida kan taba kwallo da hannu da suke ganin dan wasan Genoa ya yi.

An dakatar da Conte da Bonucci wasanni biyu ne da kuma cin su tarar Euro 10,000 sabo da cin mutuncin alkalin wasan.

Chiellini wanda shi kuma ya ji rauni baya cikin wasan amma ya je ya na yi wa jami'an wasan surutu ya sami hukuncin haramcin wasa daya haka shi maVucinic an yi masa irin wannan hukunci.

Kocin na Juventus ya ce ''muna yin aiki tukuru tsawon sati kuma adalci muke so''.

Ya ce ''zan yarda idan alkalin wasa ya ce bai gani ba, amma ya ce ba fanareti ba ce , wannan ba wasan kwallon kafa ba ne''.

Karin bayani